Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Ma’aikatan Npower sun kai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kotu kan hakkokinsu da ba’a kammala biyansu ba

Ma’aikatan N-power sun kai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kotun da’ar ma’aikata inda suke neman hakkinsu na shekara guda da ba’a biyasu ba.

Lauyan ma’aikatan N-power dinne me suna, Barrister A. A. Hikima ya shigar da karar a madadinsu.

Yace wadanda ake kara sun hada da ministan jin kai, da babban lauyan gwamnati da akanta Janar na gwamnati da kuma shugaban hukumar ta N-Power, Mr. Akindele Egbuwalo

Ma’aikatan na N-Power sun ce ba’a biyasu hakkokinsu na tsakanin October 2022 da September 2023 ba.

Sun ce duk da gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin amma su dai sun yi aikinsu dan haka ya kamata a biyasu.

Karanta Wannan  Da Duminsa: A karshe dai Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukaminsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *