
Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar Manchester United ta kori Ruben Amorim a matsayin kocinta.
Hakan na zuwane bayan da ya kwashe watanni 14 yana matsayin kocin Kungiyar.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin dan kasar Portugal din me shekaru 40 da kungiyar a ‘yan kwanakinnan.
Manchester United dai a yanzu tana matsayi na 6 akan teburin Premier league.
Manchester United ta sanar da Darren Fletcher a matsayin kocin wucin gadi.
