Friday, July 17
Shadow

Da Duminsa: Manchester United ta kori Ruben Amorim a matsayin kocinta

Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar Manchester United ta kori Ruben Amorim a matsayin kocinta.

Hakan na zuwane bayan da ya kwashe watanni 14 yana matsayin kocin Kungiyar.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin dan kasar Portugal din me shekaru 40 da kungiyar a ‘yan kwanakinnan.

Manchester United dai a yanzu tana matsayi na 6 akan teburin Premier league.

Manchester United ta sanar da Darren Fletcher a matsayin kocin wucin gadi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda matasan Daura suka rika yàgà Fastar Rarara yayin da ake masa Nadin Sarauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *