
Rahotanni daga jihar Bayelsa na cewa, Mataimakin Gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa.
An garzaya dashi FMC dake Yenagoa inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rigamu gidan gaskiya.
Ya fadi ne da misalin karfe 1:30 na rana inda na kusa dashi suka ce hakan na da alaka da yawan aikin da yake yi.