
Rahotonni nata kara karfi kan shirin komawar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC.
Sabbin Rahotannin da ake samu shine cewa nan da ranar Litinin in Allah ya kaimu, Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance zai koma jam’iyyar APC.
Hakan na zuwane yayin da siyasar Kano ke ci gaba da daukar Dumi.
Ana ganin wannan komawar ta Gwamna Abba jam’iyyar APC zata iya kawo baraka tsakaninsa da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.