
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika da sunan Janar Christopher Musa ga majalisar Dattijai dan su tantanceshi a matsayin ministan tsaro.
A cikin wasikar da shugaba Tinubu ya aikawa kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya bayyana cewa yana son janar Christopher Musa ya maye gurbin Muhammad Abubakar Badaru a matsayin Ministan tsaro.
A jiya litinin ne dai Muhammad Badaru Abubakar ya ajiye mukaminsa a matsayin Ministan tsaro inda ya ce baya jin dadi.
Janar Christopher Musa na da shekaru 58 a Duniya kuma ya nuna bajinta a aikin soja sosai inda ya samu kyautukan karramawa da yawa.