Sunday, May 25
Shadow

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya bayar da Umarnin a dauki matasa 130,000 aiki dan su shiga daji su gama da ‘yan Bìndìgà da ake fama dasu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron dazuka a ƙasar baki ɗaya, domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a Najeriya.

A karkashin wannan shiri, za a ɗauki sama da masu tsaro 130,000 da za su kasance da kayan yaƙi da horo na musamman domin kare dazukan ƙasar guda 1,129.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, wanda ya wallafa ta a shafinsa na X.

Sanarwar ta ce “Wannan mataki na tsaro an amince da shi ne yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar ranar Litinin.’

Karanta Wannan  Mu Rungumi Tsarin Amfani Da CNG A Motocinmu Maimakon Man Fetur Za Mu Sauki

“A cikin wannan tsari, shugaba Tinubu ya umurci kowace jiha da ta ɗauki ma’aikata tsakanin 2,000 zuwa 5,000 domin zama masu tsaron daji, dangane da ƙarfin kuɗin jiharsu.” in ji sanarwar.

Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da kuma ma’aikatar kula da muhalli ne za su sa ido kan aikin ɗaukar masu tsaron da horar da su domin tabbatar da cewa sun samu cikakken shiri da kayan aiki na zamani da ya kamata.

Babban aikin da ake sa ran masu tsaron dajin za su yi shi ne fatattakar masu tayar da ƙayar baya da miyagu da suka fake a cikin dazuka suna aikata laifuka.

Karanta Wannan  Matatar man fetur din Dangote zata fara fitar da man fetur din zuwa kasashen Africa guda 7

Sanarwar ta ce “Shugaba Tinubu ya jaddada cewa dole ne a horas da su sosai kuma a ba su makamai masu ƙarfi domin su iya kare ƙasar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *