
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai mayar da Gwamna Simi Fubara na jihar Rivers kan mukaminsa na gwamnan jihar.
Saidai an gindayawa gwamnan Sharuda kamar haka:
Ba zai sake tsayawa takarar gwamnan ba a zaben shekarar 2027.
Zai yadda Wike ya tsayar da ‘yan takarar shuwagabannin kananan hukumomi 23 dake fadin jihar.
Hakanan ya yadda ya biya ‘yan majalisar jihar dakewa Wike Biyanna su 27 hakkokinsu da ya dakatar, idan ya yadda da hakan, ‘yan majalisar ba zasu yi yunkurin tsigeshi ba.