
Rahotanni na cewa shugaban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, Bayo Ojulari ya halarci taron da kamfanin ya shirya a Legas inda aka ganshi yana gabatar da jawabi ta Zoom.
Hakan na zuwane yayin da ake rade-radin cewa an koreshi ko kuma za’a koreshi daga aiki inda wasu rahotannin ke cewa Tuni ma EFCC ta fara bincikensa.
Rahotanni sun ce duk wannan dambarwa ta sako Asali ne daga zargin da akewa shugaban kamfanin NNPCL din ne da aiki da surukin Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Abdullahi Bashir Haske inda ake zargin Shugaban NNPCL sun gudanar da kasuwanci da kamfanin AA&R Investment Group wanda na surukin Atikunne.
NNPCL ta turawa kamfanin Miliyoyin kudade wanda suka sa EFCC ta fara binciken huldar inda aka fara zargin shugaban kamfanin na NNPCL da karfafa ‘yan Adawa ta hanyar basu kudi.
Hakan yasa ake son a cireshi daga mukaminshi.
Saidai Wasu rahotanni sun ce matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta hana a cireshi daga kan kujerar.
Hakanan Majiyar Peoplesgazette ta bayyana cewa, wasu ma’aikatan NNPCL sun sanar da ita cewa sunga Bashir Ojulari ya koma bakin aiki a yau, Litinin.