
Abubakar Malami, wanda ya yi Ministan Shari’a a mulkin Buhari, ya baiyana dacewar tasa ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ya kuma wallafa a shafinsa na facebook.
Ya ce gwamnatin APC ta gaza wajen magance matsalolin talauci da tsaro a karkashin gwamnatin Tinubu, inda ya ce gwamnatin ta fi maida hankali kan harkokin siyasa maimakon magance matsalolin ƙasa.