
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar ‘yansandan Farin kaya ta DSS na shirin sake kama tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami da zarar an bayar da belinsa.
Malami ne ya bayyana hakan ta bakin me magana da yawunsa, Muhammed Bello Doka.
Yace DSS na shirin yi masa wannan abu da ya kira take hakinsa ne bayan da kotu ta bayar da belinsa.
Malami yayi zargin cewa, DSS sun dana tarko akansa suna jiran a bayar da belinsa su sake chafkeshi.