Friday, August 7
Shadow

Da Duminsa: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai ba zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta rahoton dake cewa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba a shekarar 2027.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane ta bakin dan uwansa, Azibaola Robert inda yace Jonathan bai ce zai tsaya takarar shugaban kasa ba ko ba zai tsaya ba.

Hakan na zuwane yayin da PDP ke cewa tana son tsayar da ko dai Goodluck Jonathan ko Peter Obi takarar shugaban kasa a 2027.

Rahotanni sun ce tuni Goodluck Jonathan ya fara tuntubar manyan mutane a kasarnan kan tsayawa takarar shugaban kasar.

Karanta Wannan  Kalli, Anata Allah Wadai da mawaki Bilal Villah bayan da ya je Ka'aba ya daga Wakar da yayi da Naziru Sarkin Waka, yana rokon Allah ya sa mata Albarka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *