
Bayo Onanuga watau me magana da yawun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya soki taohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.
Onanuga ya yi maganane akan wani Bidiyon yakin neman zaben Buhari da aka wallafa wanda yayi a Ibadan.
Onanuga yace, Masu cewa, Tinubu be wa Buhari komai ba ko kuma kuri’u Miliyan 12 na Buhari ne suka sa ya zama shugaban kasa, to ga wannan Bidiyon.

Saidai da yawa an yi caa akansa inda ake ta Allah wadai da abinda ya rubuta inda asu ke cewa, ya bari a binne Buharin ma tukunna mana.
Da suka ta yi yawa dai, Bayo Onanuga ya goge abinda ya rubuta.
Saidai duk da haka wasu na ganin cewa kamata yayi a canja masa wajan aiki ko kuma a koreshi gaba daya dan watarana zai saka shugaban kasar a matsala.