
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, nan da ranar 18 ga watan Satumba Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara zai koma bakin aikinsa tare da ‘yan majalisar jihar.
Wike ya bayyana hakane bayan ya kada kuri’ar sa a zaben kananan hukumomi da ake a jihar ta Rivers Ranar Asabar.
Wike ya kada kuri’ar sa a rumfar zabe me lamba 7 a mazabar ,ward 9 dake yankin Rumuepirikom na karamar hukumar Obio-Akpor.
Wike yace an yi zaben lami lafiya.
Yace nan da ranar 18 ga watan Satumba mulkin karta kwana zai kare kuma Gwamnan jihar Simi Fubara da ‘yan majalisar jihar zasu dawo bakin aiki