
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan Bindiga da suka yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar bautar kasa, Janar Maharazu Tsiga sun sakoshi.
An sakoshi ne bayan shafe kwanaki 22 a hannun masu garkuwa da mutanen, Rahoton yace wata majiya tace an sakoshi kuma yana wani asibiti da ba’a bayyana sunansa ba yana jinya.
A ranar 6th February 2025 ne ‘yan Bindigar suka dira a gidansa suka yi garkuwa dashi tare da jikkata mutane 2 sannan daya daga cikin ‘yan Bindigar ya mutu bayan da wani dan Bindigar ya harbeshi bisa kuskure.
A baya dai hutudole ya jiyo cewa ‘yan Bindigar sun nemi kudin fansa Naira Miliyan 250 kamin sakin tsohon sojan.
Saidai zuwa yanzu hukumomin tsaro a jihar basu ce uffan ba kan lamarin.