
Rahotanni daga jihar Filato na cewa, zanga-zanga ta barke a babban birnin jihar watau, Jos saboda yawaitar kashe-kashen ‘yan Asalin Jihar da ake zargin ‘yan Bindiga Fulani da aikatawa.
Babban Limamin kirista, Rev. Polycarp Lubo ne ya jagoranci zanga-zangar wadda aka fara ta daga Titin Fawvwei Junction wanda hakan ya kawo tsaikon ababen hawa.
Daya daga cikin masu zanga-zangar me suna Gyang Dalyop ya shaidawa kafar Punchng cewa, sun fito ne saboda basa jin dadin abinda ke faruwa na kashe-kashen a garuruwansu.
Itama wata me suna Hannatu Philip tace suna kira ga hukumomi su dauki matakan kawo karshen lamarin kamin ya kazance.
A wani lamari me alaka da wannan, Hutudole ya kawo muku cewa, a yau ne ake sa ran mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar.