
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince a sake bude wata Depot watau makarantar horas da sojoji a Bakaliki dake jihar Ebonyi.
Shugaban sojojin Najeriya, Lt. General Waidi Shuaibu ne ya bayyana haka a Zaria wajan yaye sabbin kurtan sojoji guda 3,439 da aka yi ranar Asabar.
Yace wannan bude sabon depot zai baiwa sojojin damar daukar karin sojoji da zasu samar da tsari a Fadin Najeriya.
Zuwa yanzu kenan yawan Depot din horas da sojoji da ake dasu a fadin Najeriya sun kai 3.
- Kaduna
- Osogbo
- Abakaliki