Saturday, August 8
Shadow

Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince a sake Bude Depot (Makarantar Horas da sojoji) a Abakaliki

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince a sake bude wata Depot watau makarantar horas da sojoji a Bakaliki dake jihar Ebonyi.

Shugaban sojojin Najeriya, Lt. General Waidi Shuaibu ne ya bayyana haka a Zaria wajan yaye sabbin kurtan sojoji guda 3,439 da aka yi ranar Asabar.

Yace wannan bude sabon depot zai baiwa sojojin damar daukar karin sojoji da zasu samar da tsari a Fadin Najeriya.

Zuwa yanzu kenan yawan Depot din horas da sojoji da ake dasu a fadin Najeriya sun kai 3.

  • Kaduna
  • ⁠Osogbo
  • ⁠Abakaliki
Karanta Wannan  Da Duminsa: Wike ya bayyana cewa ranar 18 ga watan September Gwamnan Jihar Rivers, Simi Fubara da majalisar jihar zasu koma bakin aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *