
!A yayin da shirye-Shirye suka yi nisa kan cewa, Abba Kabir Yusuf, gwamnan Kano da aka fi sani da Abba Gida-Gida na shirin komawa jam’iyyar APC.
Shi kuma jagoran Tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar ADC.
Kafar Thisday tace Kwankwaso na tattaunawa da jam’iyyar ADC inda yake shirin hadewa da su Atiku da Obi.
Dama dai Atiku ne yazo na 2 inda Obi ya zo na 3, Kwankwaso kuma ya zo na 4 a zaben shugaban kasa na shekarar 2023 da ya gabata.
Ana tsammanin idan wadannan manyan ‘yan Adawa suka hade waje daya duk da cewa jam’iyya me mulki na da gwamnoni 28 zasu iya bata wuta.