
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya daga kasar Brazil inda yaje halartar taron ci gaban kasashen Afrika.
Shugaba Tinubu ya taso daga kasar Brazil da misalin karfe 12 na kasar ranar Laraba, inda ya zo Najeriya ranar Alhamis kamar yanda me magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya bayyana.
Manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi shugaban kasar a filin jirgin sama na Abuja.