
Rahotanni daga S&P Global sun ce Attajirin Najeriya, Aliko Dangote zai fara hako danyen man Fetur.
Rahotan yace Dangote ya ari wasu rijiyoyin mai da ake kira da 71 da 72 wanda kamin karshe shekarar da muke ciki zasu fara hakar danyen man fetur din.
Rahoton yace Rijiyoyin man zasu rika samar da ganga 40,000 ne a kowace rana.
Wannan ci gaba karine kan matatar man fetur da yanzu haka Dangote ke da ita.