
Tsohon Ministan matasa sa wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa ko da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dansa Seyi zai baiwa shugaban hukumar zaben me zaman kanta INEC ba zai ci zaben shekarar 2027 ba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Sunnews.
Yace Tinubu ya ja dagar yaki da mutanen Najeriya saboda jefasu a halin yunwa da yayi wanda ba’a taba samun irin hakan ba a tarihin Najeriya.
Dalung yace ko da tururuwar da ake ta shiga APC ba wai dan farin jinin shugaba Tinubu bane, ana yi ne saboda kare muradun siyasa da kuma tsoron kamu.