Friday, September 11
Shadow

Da gangan Tinubu ya jefa ‘yan Najeriya cikin Yunwa, kuma irin yanda ake kulle dashi ko dansa Seyi sai baiwa shugaban hukumar zabe INEC ba zai ci zaben shekarar 2027 ba>>Inji Solomon Dalung

Tsohon Ministan matasa sa wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa ko da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dansa Seyi zai baiwa shugaban hukumar zaben me zaman kanta INEC ba zai ci zaben shekarar 2027 ba.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Sunnews.

Yace Tinubu ya ja dagar yaki da mutanen Najeriya saboda jefasu a halin yunwa da yayi wanda ba’a taba samun irin hakan ba a tarihin Najeriya.

Dalung yace ko da tururuwar da ake ta shiga APC ba wai dan farin jinin shugaba Tinubu bane, ana yi ne saboda kare muradun siyasa da kuma tsoron kamu.

Karanta Wannan  "Wallahi yanzu haka in da zan bayar da duk abin da na mallaka don in koma gida zan yi hakan, idan na koma gida sai na zuba ruwa a ƙasa na sha, na yi sujada don gode wa Ubangiji." Inji Matashin Najeriya dake shan Wahala A Kasar Libya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *