Masoyan dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo musamman Musulmai sai doki suke dan sanin cewa wai da gaske ya musulunta?
Hakan bai rasa nasaba da kasancewarsa yana buga kwallo a kasar Saudiyya wadda kasa ce me tsarki ga Musulunci.
Musuluntar Cristiano Ronaldo zata dauki hankula sosai a tsakanin masoyansa da wadanda ma ba masoyansa ba.
A bayanan da muke dasu a yayin wannan rubutu, babu wata sahihiyar kafa data tabbatar da cewa, Cristiano Ronaldo ya musulunta.
Saidai muna fatan Allah yasa nan gaba ya musulunta.