Friday, January 16
Shadow

Da gaske Sarki Sanusi II ne zai yiwa Mariya Aminu Dantata sallar Gawa? Ji bayani dalla-dalla

Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne zai yiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah a birnin Madina.

Hakan na zuwane yayin da rahotanni ke cewa, Sarki Aminu Ado Bayero ma yace Santata ya bar masa wasiyyar cewa shine zai masa sallah.

A yanzu dai gawar marigayi Aminu Dantata ta isa Birnin Madina kuma ana jiran mahukunta birnin ne su bayyana lokacin da za’a masa sallah.

A hukumance, ba’a sanar da wanene zaiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo:Malaman Izala na ta yabon Sheikh Maqari saboda kalaman da yayi akan Mafarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *