Wednesday, April 15
Shadow

Da gaske Sarki Sanusi II ne zai yiwa Mariya Aminu Dantata sallar Gawa? Ji bayani dalla-dalla

Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne zai yiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah a birnin Madina.

Hakan na zuwane yayin da rahotanni ke cewa, Sarki Aminu Ado Bayero ma yace Santata ya bar masa wasiyyar cewa shine zai masa sallah.

A yanzu dai gawar marigayi Aminu Dantata ta isa Birnin Madina kuma ana jiran mahukunta birnin ne su bayyana lokacin da za’a masa sallah.

A hukumance, ba’a sanar da wanene zaiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah ba.

Karanta Wannan  Tinubu Akwai Zalamar Mulki, Yanzu duk wahalar rayuwa da matsalar tsaro da sauransu da 'yan Najeriya ke ciki bai dameshi ba, zarcewa akan kujerar mulki ce a gabanashi? Inji Jam'iyyar PRP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *