
A karon farko cikin makonni da dama, Ministan Harkokin Wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana wa BBC dalilin rigimar da suka yi tsakaninsa da Gwamnan jiharsa ta Bauchi da kuma mataimakin Gwamnan.
Tun a baya wasu rahotanni sun ce an samu hatsaniya ne tsakanin Ministan da Gwamna Bala Mohammed, Kauran Bauchi inda har mataimakin gwamnan ya yi yunkurin marin Ministan.
Lamarin dai ya faru ne ranar Juma’a 19 ga watan Afirilun nan, lokacin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ke wata ziyara a jihar ta Bauchi.
A tattaunawarsa da BBC, Ministan ya yi karin haske kan abin da ya haddasa rashin jituwa tsakaninsu har ta kai su ga sa-in-sa.
Ministan ya ce ba kamar yadda wasu ke yadawa ba cewa da mataimakin gwamna suka yi hatsaniya, da ainahin shi gwamnan ne abin ya fara, a lokacin da suna tafiya da mataimakin shugaban kasa tare a cikin motar bas lokacin da mataimakin shugaban ya kai ziyara jihar.
‘Muna tafiya ne a cikin mota na raka mataimakin shugaban kasar ziyara jihar Bauchi, mataimakin shugaban kasa ya yi min magana, gwamna da yake zaune a gefensa ya sa baki cikin maganar wanda ba da shi ake maganar ba.” Ya ce.
Ya kara da cewa: ”Bayan haka kuma ya zagi mahaifina, mahaifin nan nawa ya yi sama da shekara ashirin da mutuwa, sannan kuma bugu da kari gwamnan ya tashi ya ce zai mare ni, wanda kuma ni na ga in an kyale mu ni ban ga yadda zai iya yi min duka ba ko ya mare ni saboda haka ni ma na tashi na gwada masa tsawo.”
”Bayan haka shi ne mataimakinsa ya sheko a guje daga bayan wannan mota bas, kan cewa shi ma zai zo ya mare ni, amma bai iya ko karasowa ko kusa da ni ba, saboda kar ka manta cewa mataimakin shugaban kasa yana cikin wannan mota,” In ji Ministan.
Ya ce, jami’an tsaron da suke wurin ba wadanda suke Bauchi ba ne zuwa aka yi da su daga Abuja.
Tuggar ya kara da cewa, ”ko hada jiki ba mu yi da gwamnan ba, illa dai kawai ya furta cewa zai mare ni, to amma shi da kansa ya ga inda zai kai marin ma sai ya daga kai sama, don haka a nan maganar ta kare, to amma akwai dan shi gwamna da yake son katsalandan ya shiga hidimar siyasa, shi ne ya dau labari ya sa a yanar-gizo kan cewa wai mataimakin gwamna, Auwal Jatau ya mare ni.”
”Shi da kansa kuma mataimakin gwamnan da ya ga abin bai musu tasiri ba suka sake yada labari cewa a’a shi fa bai mare ni ba.” A cewar ministan.
Dangane da yadda wasu ke danganta sabanin da ke tsakanin ministan na harkokin wajen na Najeriya da kuma gwamnan na Bauchi, kan cewa Ambasada Tuggan wai yana da buri ne na tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar, shi ya sa ake samun wannan takun-saka tsakaninsu, ya yi martani da cewa:
”Ko ina da buri ko ba ni da buri idan ka duba tarihina za ka ga cewa idan lokacin fadar gaskiya ya yi ina fada kuma abin da yake faruwa ya shafi karamar hukumata da garinmu na Udubo.” In ji ministan.
Ambasada Tuggar ya ce bambancin da suka samu a kan yadda ake tafiyar da gwamnatin jihar Bauchi ne.
Ya ce : ”Kowa ya sani ana ganin yadda kusan ake ta kwace wa manoma da makiyaya gonakinsu da kasarsu da suke kiwo ana bai wa kamfanoni, su kuma kamfanonin nan suna zuwa suna ciwo bashi da sunan cewa za su zo su yi noma, za su zuba a wurin.
”To abin da yake faruwa abin takaici ne domin irin wannan in aka kwace musu gonaki ko aka kwace wa makiyayi wurin kiwo ka ga wasunsu sai su je su shiga wannan harka ta ta’addanci,” in ji ministan.
Ya ce, idan har ana yin haka ne domin cigaban jihar ne kamar yadda ake nunawa, ” to me ya sa har yanzu ba mu ga jihar Bauchi ta fi kowace jiha noma hatsi ba ko kuma yawan shanu sai ma abin komawa baya yake kara yi?”
Shi dai Tuggar da mataimakin gwamnan na Bauchi, Auwal Jatau, sun fito ne daga gundumar Sanatan yankin Bauchi ta Arewa, yankin da bai taba samar da gwamnan jihar ba tun bayan komawa mulkin dumukuradiyya a 1999.
Kuma duk da cewa shi Tuggar bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan ba a 2027, akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa yana harin kujerar.
Masu lura da al’amura na ganin cewa ministan na harkokin waje zai fafata da takwaransa ministan lafiya Farfesa Ali Pate, wanda ya bayyana cewa a shirye yake ya bauta wa al’ummar jihar, wajen neman tsaya wa jam’iyyar APC wannan takara.
Duk wanda ya samu tikitin yi wa jam’iyyar ta APC takarar gwamnan a zaben 2027 zai fafata ne da, wanda Gwamna Mohammed ya mara baya ya gaje shi wajen yi wa PDP takara.
Masu lura da siyasar jihar na ganin mataimakin gwamnan ka iya kasancewa wanda zai samu wannan gata daga gwamnan.
Shi dai minista Tuggar ga gwamnatin jihar na sa-in-sa a kan yadda ministan ke sukar gwamnan a kan matsayar kauran na bauchi kan tsarin haraji na Shugaba Tinubu, inda wannan sabani ke janyo ce-ce-ku-ce a tsakaninsu ta fannoni daban-daban.