Friday, December 5
Shadow

Da Matatar Man fetur dina bata yi nasara ba da na talauce dan da duk kadarorina bankuna zasu kwace>>Inji Dangote

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, da Matatar mansa bata yi nasara ba da duka kadarorinsa za’a kwace ya koma kauye da zama.

Yace dalili kuwa shine kadarorinsa ne ya bayar bankuna suka bashi bashin da ya gina matatar man fetur din tasa.

Dangote yace an rika kiransa ana gargadin sa cewa Gwamnati ce kadai take irin wannan aikin gina matatar man fetur din da yake yi.

Yace amma duk da haka yayi kunnen uwar shegu ya ci gaba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Tambaya: Rashin Kulawar Mijina yasa na Afkawa Alfasha, Har Ciki ya shiga, menene Mafita?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *