SAKON SHIGA SABUWAR SHEKARA ZUWA GA ‘YAN NIJERIYA
Yan uwana ƴan Nigeria,
A yayin da muka shiga 2025, ina yi wa kowa fatan alheri.
Ina fatan mun shiga shekarar da ƙafar-dama, ƙunshe da farinciki, wadata nasara, da lafiya mai ɗorewa.
Wannan sabuwar shekara da muka shiga, cike take da fatan samun ingantattun kwanaki a cikinta, kuma da yardar Allah, shekarar 2025 za ta kasance shekarar cika alkawura, da burikanmu na bai ɗaya.
Duk da cewa shekarar 2024 ta kasance ɗauke da ƙalubale mai tarin yawa ga ƙasarmu da ƴaƴanta, ina da ƙwarin gwiwar cewa sabuwar shekara za ta zo mana da ƙafar -dama.
Ƴar manuniya ta nuna cewa, juma’ar tattalin arzikin mu ta fara yin kyau tun daga larabarta ga al’ummarmu, farashin man fetur ya fara sauka sannu a hankali, mun sami rara a cinikayyar ƙasa da ƙasa har sau uku a jere, lalitar ajiyar mu ta kasashen waje itama ta ƙaru, Naira ma ta ƙara ƙarfi idan aka kwatanta ta da dalar Amurka, wannan abin a yaba ne.
An sami haɓakar hada-hadar kuɗaɗe da zuba hannayen jari na tiriliyoyin Naira wanda ya haifar da riba ga kasuwannin hannayen jarin mu, hakan na nuna kyakkywan fata ga ci gaba da tururuwar masu zuba jari a ƙasar mu, wannan ma wani abin sabunta kwarin gwiwa ne ga tattalin arzikinmu.
Sai dai har yanzu muna fuskantar ƙalubalen tsadar abinci da magunguna, kuma wannan ya kasance babban abin damuwa ga lungu da saƙon Najeriya a cikin 2024.
Amma da Yardar Allah, a cikin 2025, gwamnatinmu ta himmatu wajen yaƙi da tsadar rayuwa da hauhawar farashi ta hanyar haɓaka samar da abinci da masana’antar haɗa magunguna samfurin cikin gida, da sauran kayayyakin kiwon lafiya.
Mun ƙuduri aniyar rage hauhawar farashin kayayyaki daga kaso 34.6% zuwa 15%. Kuma da idan muka bayar da himma, da taimakon Allah, za mu cim ma wannan buri na kawo ɗauki ga al’ummarmu baki ɗaya
A cikin wannan sabuwar shekara, gwamnatina za ta ƙara ƙarfafa damar samun lamuni ga ɗaiɗaikun ƴan ƙasa, da ma wasu sassa masu mahimmanci ga inganta tattalin arzikin ƙasarmu.
Ta dalilin hakan ne gwamnatin tarayya za ta kafa sabuwar hukumar bayar da Lamuni ga ‘yan Ƙasa mai suna National Credit Guarantee Company wanda zai kula da faɗaɗa hanyoyin rage haɗari ga cibiyoyin kuɗi da kamfanoni.
Kamfanin,wanda ake sa ran zai fara aiki kafin karshen zango na biyu na sabuwar shekara, zai zamo na hadin gwiwa tsakanin wasu cibiyoyin gwamnati, irin su Bank of Industry, da Nigerian Consumer Credit Corporation, da Nigerian Sovereign Investment Agency, da Ministry of Finance Incorporated, sannan da wasu kamfanoni da cibiyoyi masu zaman kansu.
Wannan shiri zai ƙarfafa gwiwar tsarin hada-hadar kudi, da fadada hanyoyin samun lamuni, da tallafa wa wasu rukunin jama’a da basu cika samin kulawa ba kamar mata da matasa. Hakan zai haifar da ci gaba, tare da sake farfado da masana’antunmu, da inganta yanayin rayuwar al’ummarmu.
Baya da wannan, ni a karan kaina, ina sake jaddada godiya ta a gare ku bisa amincewar da kuka yi da ni har na zama shugabanku. Hakika kun yi mini karamci, kuma ba zan ba ku kunya ba, na yi alkawarin ci gaba da yi muku hidima da duk ƙarfina da zuciya ɗaya.
Za mu ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da suka dace don samar da ci gaba da wadata mai dorewa ga al’ummarmu.
Ina mai ci gaba da neman hadin kan ku da hadin gwiwa kamar kullun, don cika wannan buri da na dauko na samar da tattalin arzikin dala tiriliyan daya. Mu tsaya mu mai da hankali, kuma mu haɗa kai.
Muna kan hanya miƙaƙƙiya don gina Sabuwar ƙaƙƙarfar Najeriya wacce moriyarta za ta karaɗe kowa. Kada mu shagaltu da kiraye-kirayen wasu tsiraru da ga al’ummarmu da har yanzu suke wa komai kalĺon siyasa, suke fakewa da ƙabilanci, bangaranci ko bambancin addini.
Yan Kasa Na gari!
Ba zamu cimma burin samar da Ƙasa ta gari ba har sai mun zama ’yan ƙasa na gari masu ƙwazo da sadaukar da kai ga Nijeriya.
Kyakkyawar ɗabi’ar ƴan ƙasa da riko da gaskiya a ƙasarmu sune ginshiƙai da turakun nasarar Ajandar mu ta Sabunta Fata Na Gari. Kuma InshaAllah A cikin 2025, za mu himmatu don jaddada riko da ƙa’idodin wannan ɗabi’a, wanda shine shaidar zama ɗan ƙasa.
A zangon farko na shekarar 2025, Zan kaddamar da Sabon Daftarin Tattalin Arzikin Kasa, wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta riga ta amince da shi, Zan kuma kaddamar da wani gagarumin yaki da rashin kishin kasa, wanda zai karfafa kishin kasa da kaunar juna da zaburar da ‘yan kasa su yi tafiya tare.
Daftarin zai kuma kyautata dangantaka tsakanin gwamnati da ‘yan kasa da kuma sabunta yarda da amana da hadin gwiwa tsakanin al’ummomi daban-daban na ƙasar mu.
Duk tsafta da kyakkyawan tushe da ke ƙunshe cikin gyare-gyaren mu, za mu iya samar da sakamakon da ake bukata ne kawai idan muka samar da da kyawawan dabi’u da mutuntaka da kuma soyayya marar iyaka ga kasarmu.
Ƙungiyar Confab ta Matasa zalla za ta fara aiki ne a zangon farkon farko na 2025, da niyyar hada kan manyan gobe da zuba hannun jari a matasanmu a matsayinsu na masu gina ginshiƙin ƙasa.
Nan ba da jimawa ba ma’aikatar matasa za ta bayyana hanyoyin da za a bi domin zabar wakilan taron daga mabanbantan al’ummarmu, matasa.
Ya ku ‘yan uwa, masu albarka, ina rokon ku da ku ci gaba da yarda da kanku da yarda da ƙasarmu mai ɗimbin albarka.
Bari in yi amfani da wannan sako na sabuwar shekara, in yi kira ga gwamnoninmu da shugabannin kananan hukumominmu da su hada kai da gwamnatin tarayya, wajen yin amfani da alhairan da ake samu ta fuskar noma, da kiwo, da sake fasalin haraji don ciyar da al’ummarmu gaba.
Ina yaba wa gwamnonin da suka rungumi shirin mu na amfani da Makamashin iskar gas ta hanyar kaddamar da ababen sufuri wajen rage farashin zirga-zirgar jama’a. Ina kuma taya wadanda suka yi amfani da motoci masu amfani da wutar lantarki a matsayin wani bangare na hada-hadar makamashi na kasa mai tsafta, hakika gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da bayar da taimakon da ya dace ga jihohi.
Ina Kara Jaddada wa dukkan ‘yan kasa cewa, sadaukarwar da kuka yi wa ƙasarmu na tsayin watanni 19 ba ta tafi a banza ba, zaku fara ganin canji a watanni masu zuwa inshaAllah. tare,za mu tsaya tsayin daka, mu ci gaba da aikin gina kasar mu.
Sabuwar Shekara za ta kusantar da mu zuwa ga kyakkyawar makoma da muke fata da kuma kyakkyawar Najeriyar da muke buri.
Allah ya albarkace mu baki daya, kuma Allah Ya zaunar da kasarmu Najeriya Lafiya
Ina yi wa ilahirinku Barka da Sabuwar Shekara mai albarka, shekarar 2025!
Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Tarayyar Najeriya
Janairu 1, 2025*