Friday, December 5
Shadow

Daga yau, 1 ga watan Oktoba, hukumar shige da fici ta Najeriya zata fara kama ‘yan kasar waje dake zaune a Najeriya ba bisa ka’ida ba, ko wadanda suka shigo Najeriya ba tare da takardu ba

Rahotanni sun ce daga yau, 1 ga watan Oktoba, Hukumar kula da shige da fici ta Najeriya zasu fara kame da hukunta wadanda suka shigo Najeriya bizarsu ta kare basu fita ba da wadanda kuma suna shigo ba tare da takardu ba.

Wadanda aka kama da laifi, zasu iya fuskantar hukuncin mayar dasu kasashensu ko kuma cinsu tara.

Wanda aka kama ya dade a Najeriya tsawon watanni 3 bayan shigowa kuma takardunsa sun kare, zai biya tarar Dala $15 kullun.

Ko kuma a bashi zabin hanashi shigowa Najeriya na tsawon shekaru 2.

Sai kuma wadanda suka tsaya a Najeriya na tsawon watanni 3 zuwa shekara 1, su kuma za’a musu hukuncin biyan tarar dala $15 kullun ko kuma hanasu shigowa Najeriya na tsawon shekaru 5.

Karanta Wannan  Muguntar da El-Rufai yayi a baya ce take binsa saboda Alhaki kwikwiyo ne, Kuma ba zai yi nasara ba, saboda mutane da yawa basu yadda dashi ba saboda mayaudari ne kuma maciyin amanane>>Buba Galadima

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *