
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dakatarwar da yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ce ta hana majalisar jihar tsigeshi a matsayin gwamna.
Ya bayyana haka ta bakin lauyan Gwamnati, kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi inda yace da basu dakatar da Gwamna Fubara ba da tuni an tsigeshi.
Yace kuma da an tsigeshi da shikenan yayi batan bakatantan.
Yace amma dakatarwar ta Fubara wata dabara ce ta hana tsigeshi.
Shugaba Tinubu dai ya dakatar da Gwamna Fubara har na tsawon watanni 6.