
Rahotanni sun bayana cewa, dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa gwamnan jihar Rivers Simi Fubara na Tangal-Tangal.
Dalili kuwa sai an samu biyu bisa uku na ‘yan majalisar dattijai dana majalisar wakilai duka sun amince masa kamin wannan dakatarwa ta tabbata.
A yanzu haka rahotanni, kamar yanda jaridar TheCable ta ruwaito na cewa, wakilan shugaban kasar sai kai kawo suke a tsakanin ‘yan majalisar dan ganin sun samo kansu sun amince da dakatar da Gwamnan jihar Rivers din.
Saidai matsalar itace mafi yawanci ‘yan majalisar basa Najeriya, da yawansu sun je aikin Umrah inda wasu ke wasu kasashen.
Hakanan wata matsala itace banda ‘yan majalisar dake jam’iyyun Adawa, har wadanda ke jam’iyyar APC an samu suna nuna rashin amincewa da wannan dakatarwar da akawa Gwamnan jihar Rivers.
Hakanan wata babbar matsala itace ana bukatar sai an samu ‘yan majalisa da yawa a zaune a majalisar kamin su dauki matakin amincewa ko rashin Amincewa da wannan doka.
Saidai shuwagabannin majalisar na ta kokarin ganin sun yi zama da ‘yan majalisar dake kasashen waje ko da ta WhatsApp ne su nuna amincewarsu da wannan bukata ta shugaban kasa.
Saidai wasu ‘yan majalisar da yawa na ganin cewa, hakan ya sabawa doka dan abinda doka tace shine sai an samu ‘yan majalisar a zahiri suna zaune a majalisar ne kamin a iya daukar wannan mataki.
A jiya dai, An yi kokarin tattauna maganar a majalisar wakilai saidai lamarin bai yiyu ba saboda an fara samun ‘yan majalisa da dama na nuna rashin amincewa da tsige Gwamna Fubara tun kamin ma a karanto takardar shugaban kasa ta neman dakatar da gwamnan.
A yau, Alhamis ne majalisar zata sake yin zama dan tattauna batun.