
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya amince da dokar rage awannin aiki ga ma’aikatan jihar saboda Azumin watan Ramadana.
Hakan na kunshene a cikin sanarwar da Kwamishinan haraji na jihar, Awwal Dogondaji ya fitar ga manema labarai ranar Litinin a babban birnin jihar, Birnin Kebbi.
Yace sabuwar dokar lokacib aiki shine, daga ranar Litinin zuwa alhamis, za’a rika yin aikine daga karfe 8 zuwa karfe 1 na rana.
Sannan ranar Juma’a kuma za’a rika yin aikinne daga karfe 8 zuwa karfe 12 na rana.
Yace za’a koma a ci gaba da yin aiki kamar yanda aka saba bayan watan Ramadana.
Ya jawo hankalin mutanen jihar da su dukufa da yiwa jihar dama Najeriya baki daya addu’ar zaman lafiya da ci gaba.