Saturday, May 24
Shadow

Dalilin da ya sa na koma fashi bayan na yi zaman gidan yari – Matashi

Wani matashi mai shekaru 28 da haihuwa, Olayinka Olwaseyi, da aka kama da laifin yi wa masu ababen hawa fashi a danja, ya amsa cewa ya koma aikata laifuka ne saboda rashin aikin yi.

Wanda ake zargin, wanda aka sake kama shi watanni uku bayan fitowar sa daga gidan yari, ya yi ikirarin cewa ya so ya daina aikata laifuka amma yunwa ta tilasta masa komawa ruwa.

“Ba zan koma fashi ba idan da ina da abin yi, komai kankantarsa.

“Bani da aikin yi lokacin da na fito daga gidan yari, mutane sun fara guje min, babu wanda yake so ya yi mu’amala da ni. Mutane ne su ka tilasta min na koma ruwa,” inji shi.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

An kama Olayinka ne a ranar 13 ga Mayu, 2025, a lokacin da ya ke yunkurin yi wa wani direban mota fashi a kan gadar Mile 12, Legas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama shi, inda ya ce an gan shi ya na kokarin yin fashin da misalin karfe 1:30 na safe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *