
Tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi bayanin dalilin da yasa ya kashe babban abokinsa da suka taso tare watau Mamman Batsa.
Babbangida yace yana sane da cewa, Mamman Batsa tun suna yara yana kishi da ci gaban da yake samu, yace amma duk da haka ko da ya zama shugaban kasa, sai da ya bashi ministan babban birnin tarayya Abuja, duk da yake cewa ba tare dashi akawa Buhari juyin mulki ba.
Babangida yace ko da suna makaranta da aka bashi Shugaban dalibai, Mamman Batsa bayawa umarninsa biyayya inda yakan rika ce masa ai ba wani abun azo a gani bane dan mutum ya zama shugaban dalibai.
Yace hakanan da suka shiga aikin soja ma ya rika masa hassada.
Yace A lokacin da yake shugaban kasa, bincike ya tabbatar da cewa Mamman Batsa ya shirya kifar da gwamnatinsa wanda da yayi nasara, hakan zai jefa kasar cikin rikici da zubar da jini.
Yace dole ya zabi tseratar da Najeriya maimakon tseratar da rayuwar abokinsa. Yace kuma kowa ya sani a gidan soja hukuncin yunkurin juyin mulki idan ba’a yi nasara ba kisane.
Kashe Mamman Batsa na daya daga cikin abubuwan da ake sukar Gwamnatin IBB dashi.