
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dalilin da yasa ya yafewa Maryam Sanda laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello shine ta nuna nadama sosai.
Premium times ta ruwaito cewa fadar shugaban kasar ta bayyana hakane a yayin da cece-kuce yayi yawa kan yafiyar da shugaban kasar yawa Maryam Sanda inda wasu ke cewa laifinta yayi muni sosai, bai kamata ace an yafe mata ba.
Saidai duk da haka, fadar shugaban kasar tace har yanzu ana kan duba sunayen da shugaban kasar ya yafewa kamin sakinsu.