Thursday, September 17
Shadow

An sace wayar Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, an sace wayar Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar.

Lamarin ya farune ranar Alhamis kamar yanda kafar Leadership ta ruwaito inda tace an sace wayar Kwamishinan, Hon. Barrister Sule Shu’aibu (SAN). Ne a wajan wani taro da ya halarta.

Zuwa yanzu dai ba’a bayyana sunan barawon da yayi satar ba.

Lamarin ya baiwa mutane mamaki ganin cewa a ko da yaushe Kwamishinan na tare da jami’an tsaro ko ta yaya har barawon ya samu damar sace masa waya?

Har yanzu hukumomi a jihar Kaduna basu fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kalli Bidiyon yanda aka Dambhace aka baiwa hammata iska tsakanin jami'an tsaron gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da jami'an tsaron da aka Jibge dan su hana Gwamnan shiga Hedikwatar Jam'iyyar PDP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *