
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya bayyana dalilan da suka sa Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bai tsallake tantancewar zama minista da majalisa ta masa ba.
Wannan martani na zuwa bayan da El-Rufai a hirar da yayi da gidan talabijin na Arise TV yace ba majalisa ce taki tantanceshi ba, Tinubu ne ya canja ra’ayi game da mukamin da yaso ya bashi.
Reno Omokri wanda a yanzu ya shiga sahun masu kare gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa majalisar tarayya ta gudanar da bincike a cikin gida da kasashen waje kan Nasir El-Rufai kuma binciken nasa bai yi kyau ba shiyasa ba’a bashi mukamin ministan ba.
Ya jero laifukan El-Rufai da suka hana a bashi mukamin ministan kamar haka:
Yace a ranar Alhamis, February 7, 2019 El-Rufai ya yiwa Turawa masu sa ido akan zabe a Najeriya barazanar cewa idan suka sake suka yi katsalandan a harkar zaben Najeriya zasu koma gida a cikin makara.
Yace a wancan lokacin Turawan sai da suka aikowa da Najeriya takarda game da maganar inda suka nuna rashin jin dadinsu.
Yace kuma ana zargin El-Rufai da hannu a kisan Kiristoci a kudancin Kaduna wanda ya fada da bakinsa cewa ya biya Fulani Makiyaya.
Yace kuma ana zargin El-Rufai da hannu a kisan sa akawa ‘yan shi’a a Zaria a ranar Asabar, December 12, 2015 wanda yayi sanadiyyar kisan ‘yan shi’a 438 da suka hada da mata da yara hadda jarirai.
Yace hakanan a lokacin da yake Gwamna, El-Rufai ya rushe gidajen abokan hamayyarsa, irin su Sulaiman Hunkuyi, Inuwa Abubakar da sauransu.
Yace hakanan akwai gidan wani dan adawar ma da aka rushe da zargin cewa, za’a yi bikin zina a cikinsa amma daga baya aka gano karyane amma duk da haka sai da aka rushe gidan.
Yace hakanan a wata ranar Asabar, January 27, 2013 El-Rufai ya taba zagin Annabi Isa(AS), sannan a ranar Juma’a, January 18, 2019 El-Rufai ya taba cewa ko da fafaroma zai zo dashi yasan Kiristoci ba zasu zabeshi ba.
Yace wadannan dalilai ne suka sa El-Rufai bai tsallake tantancewar majalisar tarayya ta zama Minista ba kuma kansa ya kamata ya zarga ba Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.
Yace kuma ba El-Rufai ne kadai bai tsallake tantancewar ba akwai Danladi Sani daga jihar Taraba sannan akwai Stella Okotete daga jihar Delta wanda suma duk basu tsallake ba.