Friday, December 5
Shadow

Dalla-Dalla Ji Dalilin da ya sa Ganduje bai je tarɓar Tinubu ba a Kano

Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bai je tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba a Kano ranar Juma’a saboda balaguron da ya yi zuwa birnin Landan, a cewar makusancinsa Muhammad Garba.

Ganduje wanda ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a watan Yuni ya shirya tafiyar ne kwana biyar kacal da saukarsa daga muƙamin, kamar yadda Muhammad Garba ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Asabar.

Tinubu ya je Kano ne domin yin ta’aziyyar attajiri Aminu Ɗantata da ya rasu a ƙarshen watan Yuni, kuma rashin ganin Ganduje a wurin ya jawo cecekuce tsakanin magoya baya da ‘yan’adawa a jihar.

“Ba kamar abin da ake yaɗawa ba cewa da gangan ya ƙi zuwa ko kuma ba shi da lafiya, Ganduje ya je Landan ne saboda tafiyar da aka shirya da daɗewa tun kafin ziyarar,” in ji sanarwar.

Karanta Wannan  Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya janyo ambaliya a Makka

Garba ya tabbatar cewa an sanar da Ganduje game da ziyarar shugaban ƙasar, “kuma ya yi niyyar zuwa amma duk ƙoƙarin da ya yi na sauya lokacin tashin jirginsa bai yi nasara ba”.

“Sauka daga muƙamin da Ganduje ya yi bai shafi alaƙarsa da Tinubu ba ko kaɗan, wadda ta ginu tsawon shekaru cikin girmamawa da buƙata irin ta siyasa,” a cewar Garba.

Garba wanda tsohon kwamashinan yaɗa labarai ne a gwamnatin Ganduje, bai bayyana abin da mai gidan nasa ya je yi Landan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *