Dan majalisar dokokin jihar Kano ya fice daga NNPP zuwa APC.

Dan majalisar dokoki ta jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.
A cikin wata wasikar murabus da ya aike wa Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, Hon. Masu ya bayyana rikice-rikicen cikin gida da shari’o’in da suka addabi NNPP a matsayin babban dalilinsa na barin jam’iyyar.
Kakakin Majalisar, wanda ya karanta wasikar a zauren majalisar yayin zaman ranar Litinin, ya sanar da murabus din Masu daga jam’iyyar tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, tare da tabbatar da cikakken biyayyarsa ga jagorancin jam’iyyar APC daga matakin mazaba har zuwa jiha da kasa baki daya.
Dan majalisar ya kara da cewa wasu mutane da dama daga matakin jiha da na kasa suna ikirarin shugabancin NNPP, inda ya ambaci Dr. Suleiman Hashim Dungurawa da Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa a matakin jiha, yayin da Dr. Ahmed Ajuji da Dr. Agbo Major ke ikirarin zama shugabannin jam’iyyar a matakin kasa, lamarin da ya haifar da shari’o’i a kotu wanda ke gurgunta jam’iyyar.