Friday, December 5
Shadow

Dan majalisar Tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya jefar da Jar Hula NNPP ya koma jam’iyyar APC

Dan majalisar wakilai ta tarayya, Abdulmumin Jibrin Kofa dake wakiltar mazabun Kiru/Bebeji ya bar jam’iyyar NNPP ya kpma jam’iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a sakon da ya fitar a shafinsa na sada zumunta.

Hakan na zuwane watanni 2 bayan da jam’iyyar NNPP ta koreshi bisa zargin yana mata zagon kasa da kuma kin biyan kudaden harajin jam’iyyar.

Komawarsa APC bata zowa mutane da bazata ba musamman lura da yanda yake da alaka me kyau da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ya bayyana cewa yana goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027 sannan kuma yace malamai 2000 ne sukawa shugaba Tinubu da Najeriya addu’a a mazabarsa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: An fara yiwa Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami yakin neman zama gwamnan Gombe a 2027, ji wakar da aka rera masa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *