Monday, December 16
Shadow

Dan Wasa Mbappe Ya Ji Rauni A Karan Hanci A Wasan Da Suka Yi Da Austria

Kylian Mbappe ya ji rauni a karan hanci a wasan farko da Faransa ta yi a cikin rukuni na hudu a Euro 2024, amma baya bukatar tiyatar gaggawa.

Wadda ta yi ta biyu a kofin duniya a Qatar a shekarar 2022 ta yi nasarar cin Austria 1-0, bayan da Maximilian Wober ya ci gida a minti na 38 a karawar farko a cikin rukuni.

An sanar da cewar ba sai an yi wa sabon dan kwallon Real Madrid tiyata da wuri ba, wanda ake fatan zai murmure a kan lokaci.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta sanar cewar za ta samar da kariyar fuska ga kyaftin din, amma ba ta fayyace ko zai buga wasa na biyu da Netherlands ba.

Karanta Wannan  Jami'n Dan Sandan Nijeriya Ya Rasa Ŕansa, Inda Wata Mota Ta Yi Çìki Da Shi A Shingen Bincike

Mai shekara 25, sai sauya shi aka yi a wasan da Faransa ta yi nasarar cin Austria 1-0 a ranar Litinin.

Ya kuma ji rauni ne sanadiyyar karo da ya yi da kafadar Kevin Danso, lokacin da suka ci kasuwar sama.

Daga nan ne aka dauke shi zuwa wani asibiti a Dusseldorf, wadanda suka tabbatar da girman raunin da ya ji.

Hukumar kwallon kafar Faransa ta kara da cewar ”Tuni aka sallame shi daga asibitin, har ya koma sansanin horor kasar.”

”Ta kuma ce nan da kwanaki masu zuwa za a yi masa aiki a karan hancin da ya ji rauni, amma kawo yanzu baya bukatar tiyata da gaggawa.

Karanta Wannan  'Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya'

Ranar Juma’a ne rukuni na hudu zai buga wasa na bibiyu tsakanin Netherlands da Faranasa a Red Bull Arena da na Poland da Austria a Olympiastadion.

Ranar Lahadi Netherlands ta yi nasarar doke Poland 2-1 a karawar da suka yi a filin wasa na Volksparkstadion.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *