
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya zargi shugaban Hukumar kula da man fetur ta kasa, NMDPRA Engr. Farouk Ahmed da kai ‘ya’yansa makaranta kasar Switzerland inda yace ya biya musu dala Miliyan $5.
Dangote yace wanda ke daukar Albashi ina ya samu irin wadannan kudade.
Yace koshi ‘ya’yansa ba zai biya musu irin wadannan makudan kudade ba lura da cewa a Kano akwai yaran da basa iya zuwa makaranta.
Dangote yace akwai masu neman karyashi da hana matatar man fetur dinsa yin aiki yanda ya kamata.