
Rahotanni sun ce gidajen man fetur na MRS da sauran wadanda ke sayar da man fetur din Dangote zasu fara sayar da man akan naira 739.
Hakan na zuwane bayan da Dangote ya rage farashin man da yake sayarwa daga Naira 828 zuwa Naira 699.
Rahoton yace wannan sabon farashin ka iya fara aiki nan da ranar Talata.