
Darajar hannun jari a Amurka da kuma kuɗin ƙasar Dala, ta ƙara faɗuwa, bayan da Shugaba Trump ya sake nanata sukar da yake yi wa shugaban babban bankin ƙasar.
A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara na – Truth Social, Mista Trump ya kira, shugaban bankin Jerome Powell a matsayin babban mai asara, saboda ya ƙi rage yawan kuɗin ruwa.
Wannan matsala da ke ci gaba ta sake tasowa ne a wannan karon yayin da shugabanni da jagororin harkokin kudade suke nufar babban birnin Amurka – Washington domin halartar taron Babban Bankin Duniya, da kuma Asusun Bayar da Lamuni na duniya, IMF.
Shugaban kamfanin zuba jari na kamfanin Scharf Investments, Brian Krawez, ya yi bayani kan wannan hali na kara sulmiyowar darajar hannayen jari na Amurka da kuma darajar Dalar, bayan da Shugaba Trump din ya sake bijiro da sabanin da ke tsakaninsa da shugaban babban bankin na kasarsa:
Ya ce: ”Yau ma wata mummunar rana ce ga hannayen jari. Akwai wasu sakonni na shafin sada zumunta, daga shugaban Amurka da ke barazanar korar Jay Powell, wannan ci gaba ne na rashin tabbas da haraji da manufofi da muka gani. rashin tabbas na manufa a yanzu ya ma fi yanda ya ke a lokacin annobar Covid – kuma yuwuwar korar Jay Powell, da za ta kasance abin da ba a taba gani ba – wannan na tayar da hankalin masu zuba jari a yau.”
Dambarwar kasuwanci da Shugaba Trump ya janyo, ta jefa fargaba a tattalin arziki na duniya, kuma ana ganin ita za ta mamaye tattaunawar da za a yi a babban taron na Bankin Duniya da Asusun Bayar da Lamunin na duniya da za a yi a Amurkar.