
Naira ta samu tasgaro a kasuwar Chanji inda ta fadi zuwa N1,510 akan kowace dala a jiya.
Wanan farashi yayi sama idan aka kwatanta da yanda aka kulle kasuwar a makon da ya gabata inda Nairar ke akan farashin N1,505.
Saidai a kasuwar Gwamnati Nairar tashi ta yi inda aka sayi dala akan N1,499.
Za’a iya fahimtar hakan idan aka yi la’akari da farashin da aka kulle kasuwar a makon da ya gabata na N1,500 akan kowace dala.