Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta ja kunnen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan yawan baiwa yarbawa mukami a gwamnatinsa fiye da sauran kabilun kasarnan
Sanatarwar hakan ta fito ne daga shugaban kungiyar da kuma da kuma sakataren yada labaranta Ayo Adebanjo, da Justice Faleye.
Kungiyar tace fifikon da Tinubu ke nunawa ka iya bata dangantakar dake tsakanin Yarbawa da sauran kabilun kasarnan.
Sun kuma jaddada cewa dolene Tinubu ya gyara wannan kuskure da yayi.
Kungiyar tace ba zata kwashe shekaru tana Adawa da irin wannan lamari ba a mulkin sauran shuwagabanni wanda ba yarbawa ba amma a shugabancin bayerabe ta yi shiru ba.
Kungiyar dai tace duk shuwagabannin EFCC, CBN,DSS, Army, Navy, ‘Yansanda, Customs, Immigration, Bank of Industry, Babban Lauyan Gwamnati, Alkalin Alkalai, duk Yarbawane.
Tace Garama Buhari shi duka Arewa ya fifita dake da Yankuna 3 amma shi Tinubu ba kudu ya fifita ba, Kabilar Yarbawa kadai ya fifita.
Saidai Tuni me baiwa shugaban kasa shawara kan wayar da kan ‘yan kasa, Sunday Dare ya musanta zargin cewa shugaban na fifita Yarbawa akan wanda ba yarbawa ba.