Monday, December 9
Shadow

Dattawan Yarbawa sun ja kunnen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan fifiko da yake nunawa wajan baiwa Yarbawa mukamai da yawa fiye da sauran kabilun kasarna

Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta ja kunnen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan yawan baiwa yarbawa mukami a gwamnatinsa fiye da sauran kabilun kasarnan

Sanatarwar hakan ta fito ne daga shugaban kungiyar da kuma da kuma sakataren yada labaranta Ayo Adebanjo, da Justice Faleye.

Kungiyar tace fifikon da Tinubu ke nunawa ka iya bata dangantakar dake tsakanin Yarbawa da sauran kabilun kasarnan.

Sun kuma jaddada cewa dolene Tinubu ya gyara wannan kuskure da yayi.

Kungiyar tace ba zata kwashe shekaru tana Adawa da irin wannan lamari ba a mulkin sauran shuwagabanni wanda ba yarbawa ba amma a shugabancin bayerabe ta yi shiru ba.

Karanta Wannan  Gwamnati ce zata kayyade farashin man fetur dina>>Inji Dangote

Kungiyar dai tace duk shuwagabannin EFCC, CBN,DSS, Army, Navy, ‘Yansanda, Customs, Immigration, Bank of Industry, Babban Lauyan Gwamnati, Alkalin Alkalai, duk Yarbawane.

Tace Garama Buhari shi duka Arewa ya fifita dake da Yankuna 3 amma shi Tinubu ba kudu ya fifita ba, Kabilar Yarbawa kadai ya fifita.

Saidai Tuni me baiwa shugaban kasa shawara kan wayar da kan ‘yan kasa, Sunday Dare ya musanta zargin cewa shugaban na fifita Yarbawa akan wanda ba yarbawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *