
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnati ta saka ladar Naira Miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka aka kama wadanda suka tsere daga gidan yarin Ilesa na jihar Osun.
Saidai wani shafi a Twitter wanda yake ikirarin shi daya daga cikin wadanda ake nema ne yace damfarar dala $20 kawai yayi aka kamashi.
Yace amma a aikawa Mahaifiyarsa Miliyan 5 din da aka ce an saka akan duk wanda ya taimaka aka kamasu shi kuma zai koma gidan yarin da kansa.
Saidai wasu na shakkun cewa ba shi bane.