Wednesday, January 15
Shadow

Dogarin Sanata Barau Jibrin ya rasu

Sanata Barau I. Jibrin yayi alhinin rasuwar daya daga cikin hadimansa me suna Corporal Barde Nuhu da ya rasu a hadarin mota.

Corporal Barde Nuhu ya rasune a yayin da yake kan hanyar zuwa gida jihar Naija dan ganawa da iyalansa.

Yana kan hanyar zuwa Kauyen Shata ne dake karamar hukumar Bosso a jihar ta Naija yayin da hadarin ya rutsa dashi.

Sanata Barau a sanarwar da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ismail Mudashir yace Barde hazikine sosai wajan aiki.

Yace yana mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin da kuma hukumar ‘yansandan Najeriya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda matar mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da mata 400 ke rufe fuskarta dan Kunya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *